Domin Murtala Uba
Can
take bisa kawunanmu
Sai mun xaga kai da idanuwanmu
Ta yi qoli, ba mai iya sa gannanmu
Su hango ina ta kare daga lungunnanmu
Ita ce xauke da iska don mu shaqa
Daga gareta rana ke haska mu ba mushaqqa
Hadari da girgije na nan kowace kiqa
Halitta ce ta Mafi zalaqa
Sama,
ba wasa aka yi ta
Ta wuce duk tunani na fahimta
Babu sanin iyakacinta
Sai Allahu da yake halinqinta
Ga
duniyoyi ko’ina an aje su
Ga taurari gari-gari aggaresu
Kai, ko yula da mashi Ya saka su
Kowane na bin umarnin Ubangijinsu
Allahu
Mai halitta ba irinsa
Ikonsa ya fi tunanin halittarsa
Qarfinsa ya wuce ai musunsa
Huwallazi wanda babu irinSa.