An taba bugawa a http://www.kanoonline.com/yusufadamu/
Ko’ina mutum ya kewaya a birnin Kano yanzu zai lura da wani abu guda da mamaye birnin a lokuna da lunguna. watau shaguna. Kano ta zama ko’ina shago. Kila a iya cewa ci-gaban harkokin kasuwanci ne suka kawo haka, tunda Kano cibiyar kasuwanci ce tun shekaru aru-aru. Ba za a ki hakan ba. Za a kuma lura da cewa a halin yanzu mafi yawancin masana’antun dake Kano a rufe suke, saboda haka a halin da muke ciki yanzu ba na kera abubuwa a Kano kamar yadda ake yi a da, amma ana ta gina shagunan sayar da kayayyakin da ake kerawa a Legas da Onicha.
Akan yi wa Kano kirari iri-iri ciki har da cibiyar kasuwanci, cibiyar addinin da al’adu ko ace gari ba Kano ba dajin Allah, yaro ko da me ka zo an fika. I, babu shakka Kano gari ne mai tsawon tarihi kuma wadanda suka gina Birnin Kano shekara da shekaru ba ragwaye ba ne ba kuma mutane ne masu son zuciya da hadama da kuma rashin kishi ba. Mutane ne hazikai, masu kishin birnin Kano da son kyautata bayansu. A yadda na san mutanen Kano ‘yan shekaru kadan da suka wuce, a halin yanzu sun zama kanawawa ba kanawa ba domin kuwa Kano ba ta ransu. Abin da ke ransu abin da zuciyarsu ke so. Duk wannan shimfida ce na ke yi dangane da yadda aka sa ido ganuwar birnin Kano ta zagwanye ta lalace ake kuma kokarin shareta daga doron kasa duk da irin kimbin tarihin da ta ke da shi.Saboda haka, za a lura da wani abu guda, an kusa share Ganuwar Birnin Kano daga doron kasa. Wannan shi ya fi damuna matuka gaya.
Tarihin Ganuwar Birnin Kano
Duk tsoffin birane a kasar Hausa wadanda aka kafa kafin dauloli da ma wadanda aka kafa bayan kahuwar dauloli ko bayan jihadi suna da Ganuwa. Tsofaffin birane kamar su Kwatarkwashi da Birnin ‘Yandoto da Birnin Katsina da Birnin Koga da kuma birnin Kano suna da Ganuwa. Akan gina ganuwar gari ne kuwa domin a kare gari daga hare-hare da suka yi yawa a wancan zamani. Birnin Kano ko ace Daular Birnin Kano ta sha karawa da Daular Katsina da ta Zamfara da ta Zazzau kai har ma da su Damagaram.
Domin a kare birnin da kuma jama’arsa ne a cikin karni na 12 (kusan shekaru 800 da suka wuce) aka fara gina ganuwar birnin Kano. An fara gina Ganuwar Birnin Kano a karni na goma sha biyu a zamanin Sarkin Kano Gajimasu wanda ya yi zamani a tsakankanin shekarar 1095 zuwa 1134. An kammalata a zamanin sarkin Kano Jusa. Kamar yadda Dr. Adamu Tanko na sashen labarin kasa na jami’ar Bayero ya yi bayani, katangar a zamanin ta kewaye ~angaren Dala da Gwauron Dutse ne. Har yanzu in aka je wurin kofar Mazugal za a ga burbushinta.
Daga nan sai ganuwar ta yi arewa ta bi ta Kofar Ruwa/Linkwi ta kofar Waika da kofar ansakali. Daga nan sai aka juya ganuwar ta yi gabas ta bi ta wajen kurkukun Gwauron Dutse. Ganuwar ta gangaro tayo wajen Masallacin juma’a na birni sannan ta yi wajen Asibitin Murtala ta mike ta kofar Wambai. An zagaye birnin lokacin kenan. A karni na goma sha biyar, saboda yawan jama’a da ha~akar harkokin kasuwanci, birnin Kano ya kara ha~aka. A sakamakon haka ne Sarkin Kano Muhammadu Rumfa wanda ya kara fadada ganuwar Kano. Dr. Tanko ya bayyana cewa Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya kara da’irar ganuwa da kusan kashi 51 kuma ya tayar da gidan masarautar Kano ya matso da ita dai-dai inda take a hali yanzu ta yadda ya shiga sabon birni, tunda kafin ayi hakan, inda gidan Sarki yake a halin yanzu a lokacin wajen badala ne. A wannan karon ne aka sami kofofi kamar su Gadon {aya da Dan Agundi da kuma kofar Na’isa har ganuwar ta tarar da kofar Kansakasli.
Lokaci na karshe da aka kara fadada ganuwar birnin Kano shine a karni na goma sha bakwai a zamanin sarkin Kano Muhammadu Nazaki, sarki na 28. Wani masani ya yi hasa- shen cewa Wambai Giwa shi ne ya yi wannan gagarumin aiki a lokacin da Sarki ya tafi yaki da kasar Katsina. Ganin cewa shi wambai Giwa bashi da lafiya a lokacin da aka tafi yakin, sai ya yi tunanin me zai yi ya burge Sarki in ya dawo! An ce a lokacin da aka yi wannan aiki sai da aka yanka shanu dari. To ganuwar birnin Kano da muke gani yanzu, a wannan lokaci ne aka ginata. Ba za a ce ba a kara yi mata komai ba tun daga lokacin har zuwa lokacin Jihadi. Babu ko shakka ana yi mata ya~e ana kuma kyautata ta. Wannan dalili shi ne ya sa har ta kawo yau muke ganin sauranta.
A taron Cikar Kano shekara 1000 da soma mulki, Dr. Tanko ya yi tambayar cewa da anci gaba da fadada ganuwar birnin Kano ina za ta kai a halin yanzu? Har yana cewa da kila yanzu ta kai Kura.
Ba sai an yi dogon bayani ba. Kowa zai iya fahimtar dalilin gina ganuwar gari. Kuma kamar yadda aka fada a baya, ba birnin Kano ne kawai ke da ganuwa ba. Manyan biranen kasar Hausa kamar su Katsina da Zazzau da Sakkwato duk suna da ita, to amma in anje yau kila sai dai a tarar da kaofofi kawai ba ganuwa. {anana garuruwa ma kamar su Kausani a karamar hukumar Wudil suna da ganuwa. Ana kyautata zaton cewa kafin zuwan turawa akwai garuruwa fiye da dari masu ganuwa a kasar hausa, amma yanzu duk sun zama tarihi saboda sakaci da rashin kishin tushen da mutum ya fito.
Inda za a iya nuna mana majigin yadda ganuwowin birane suke a kasar Hausa kafin zuwan Turawa da an burge mu da kuma mun fahimci cewa kakanninmu wayayyu ne kuma masu basira da fusaha. Ku duba yadda Turawan Mulkin mallaka suka dauki bakar fata a matsayin koma-bayan halitta, amma da suka zo cin Kano da yakI sai da suka sara wa kakanninmu.Lord Lugard a 1903 da ya zo Kano, ga ruhoton da ya aika Ingila dangane da Badalar birnin Kano.“lokacin da dakaranmu suka iso Kano sun iske wata babbar Katanga mai matukar kwari wadda ta kewayen birnin. Wannan Katanga ta kwancewa hafsoshinmu kai domin ba su yi tsammanin ganin wani abu kamar haka ba. Ni kai na ban ta~a gani ko tunanin zan ga wani abu irin wannan a Afirka ba. Ganuwar ta kai mil goma sha daya tana da kofofi guda goma sha uku (13). Daga bisani an auna ta an ga cewa tsawonta ya kai kafa 30 zuwa kafa 50, fadinta kuma kafa 40 ne. Akwai kududdufai a gabanta da bayanta”
Makomar Ganuwar Birnin Kano
Tun daga farko-farkon shekara ta dubu biyu na fara rubuce-rubuce akan matsayin Ganuwar Birnin Kano a halin yanzu, an buga wasu a jaridar jihar Kano watau Triumph. Ba komai ya sa na soma rubuce-rubuce ba sai don ganin muhimmancin yin haka, a matsayina na malamin Jami’a kuma marubuci, ina ganin ta hanyar rubutu ne hanya mafi sauki a gareni in isar da sako ga wadanda abin ya shafa, wadanda za su iya yin wani abu da kuma wadanda ba za su iya yin komai ba.
Duk wanda ya zagaya birnin Kano yanzu zai lura da cewa akwai alamar cewa a wani zamani da ya wuce tsohon birnin a kewaye yake da ganuwa. Ita wannan ganuwa tana daya daga cikin muhimman kayan tarihi da Kano ta dauri ta bar mana. Sai kuma abin takaici shine gani yadda aka yi sakaci har ganuwar ta zagwanye. A wasu wuraren ma babu ita babu alamarta, misali daga kofar Nassarawa (ta inda Nasara suka ci Kano) zuwa kofar mata babu ganuwa. Amma daga kofar Nassarawan zuwa har kofar Waika da sauran alamunta. Abin tambaya anan shi ne laifin wanene?
Zuwan masu Jihadi Kano bai sa an wulakanta badala ba, zuwan Turawan Mulkin mallaka bai sa an yi watsi da kula da badala ba. Lalacewar badala ya somo ne bayn tafiyar Turawan Mulki, bayan mulki ya dawo hannunmu. Wannan ba karamin abin bakin ciki ba ne. Ta kai yau kowa na da ikon sare badala ya yi bulo da kasar ko kuma ya yi gini a bisanta kuma babu wanda ya isa ya ce masa me yasa. Ta kai cewa harabar badalar ta inda mai wucewa zai iya hangenta akalla ya tuna cewa kakannin mu sun yi abin a zo a gani hukumomin Jihar Kano, wadanda hakkin kare martabar mutanen Kano ke hannunsu sun rabe wurare an yi manya-manyan gine-ginen shaguna da wuraren ajiye ko sayar da motoci. Duba daga kofar Nassarawa zuwa kofar Kabuga. Abin tambaya anan shin me Masarautar Kano ke yi akan wannan barnatar da kayan tarihi da ake yi? Me hukumar gidaje da wuraren tarihi ta kasa take yi? Kuma me hukumar tarihi da al’adu na jihar Kano ke yi? Sannan kuma me mutanen cikin birnin Kano wadanda kakanninsu ne suka gina ganuwar, suke yi akan hakan?
To, ba za a ce ba a yin komai ba, domin na sadu na shugaban hukumar gidaje da wuraren tarihi ta kasa na kusa tattauna da shi akan matsalar. Malam Musa Humbolu ya yi mani bayanin cewa Masarautar Kano, musamman mai Martaba Sarkin Kano suna yin iya bakin kokarinsu, sai dai an fi karfinsu ne. amma ya koka akan cewa wane da wanen Kano ne abin bai dame su ba kuma sune ke daure gindin ~annata badalar Kano.
To a gaskiya da sake. Bai kamata mutane su zuba ido ana kasha mana tarihi ba. In dai har za a rika cika baki ana cewa gari ba Kano ba dajin Allah, yaro ko da me ka zo an fi ka kuma Kano Jallah ce babbar Hausa, amma a kasa kare mata kayan tarihinta a gaskiya an ji kunya. Duk manyan mu sun zagaya duniya sun kuma ga abubuwan tarihi da al’umu suka bari, sun kuma san muhimmancin adana kaya da wuraren tarihi, amma a ce sun kasa cewa uffan akan kyautata badalar Kano. A kasar Hausa gaba daya fa ba mu da wasu muhimman kayan tarihi da ya wuce badala. Bayan Rijiyar Kusugu da Hubbaren Shehu da marina me muke da shi wanda zai nuna ayyukan kakanninmu?
In har Turawa duk da wayewar kansu ta zamani za su rika adana kayan tarihinsu don me mu ba za mu yi ba. Lokacn da na je Ingila a 1998 na je wani wuri da ake kira Stonehenge. Na sha karanta tarihin wajen a littatafai kuma Allah Ya nufe ni da zuwa wurin. Duwatsu ne aka yi a zagaye, sai masana sun ce an gina wurin ne shekaru 5000 da suka wuce. Duk da cewa an dan ta~a tsarin duwatsub har yanzu wurin na nan a killace kuma mutane daga ko’ina cikin duniya suna zuwa kullun suna gani. Ana kar~ar kudin shiga da kudin kuma ake ci-gaba da kyautat wurin, bayan gudunmuwar hukuma da masu kudI da sauran jama’a.
Kammalawa
Saboda haka, lokaci ya yi da mutanen Kano za su fara tunanin dakatar da rushe ko kare badalar Kano da kuma fara shirye-shiryen tada ita. Misali, in an yi niyyar tada badalar Kano ba abinda zai hana. A fara daga kofar Nassarawa zuwa kofar Ruwa. Daga bisani a tada sauran ~angaorin. Wannan ba abu ne da zai gagara ba sai dai in ba a yi niyya ba. Rashin niyya kuma mun san ba zai kai mu ga nasara ba.
Idan da gwamnatin Jihar Kano tare da Masarautar Kano da mutanen Kano za su daura niyya tada badala, na tabbata Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyi da hukumomin kas ashen waje ba za su kI taimakawa ba.
Amma mu kan mun yi kudurin ci gaba da fafutukar kare badala da kokarin tada ita matukar rayuwarmu kuma ko ba wanda zai yi wani abu a halin yanzu mu, mun fita hakkI tunda mun fadakar mun yi nasiha mun kuma ilmantar. Saura da me kila a wasu shekaru masu zuwa za a sami wani Sarki Gajimasun ko Jusa ko Muhammadu Rumfa, ko ma a sami wani Wambai Giwan da zai tada badalar Kano, daga nan kuma a tada na sauran biranen {asar Hausa. Muna fatan daga wannan rubutu mutane za su fara tsumuwa.