Tuesday, October 22, 2013


Dalilan Yajin Aikin ASUU

 

Koyaushe a ka ce malaman jami’a na yajin aiki mutane kan faxi albarkacin bakinsu. Wasu su goyi bayanmu wasu kuma su goyi bayan gwamnati. Wasu kuma su tsaya a tsaka-tsaki suna ganin laifin kowa. A wannan karo ma haka muka tsincin kanmu.

Da yawa mutane na mamakin me ya sa muka xauki yajin aiki da muhimmancin da har wasu suna ganin cewa da mun nemi abu an hana mu sai mu tafi yajin aiki. Wannan dalili ne ya san a ga ya dace a matsayina na malamin jami’a in yi wa jama’ar Nijeriya bayani akan halin da muka tsinci kanmu a wannan karo ko ma yi wa juna adalci.

Yajin aikin Malaman Jami’a da ya fara shahara shi ne wanda aka yi lokacin mulkin soja na Janar Babangida qarqashin shugabanci Dk. Attahiru Jega a 1992. Yajin aiki ne da aka yi fiye da wata shida ana yi har ya jawo an rufe dukkan jami’o’in Nijeriya. A wannan lokacin, bayan tsayar da albashin malamai da aka yi har ma ta kai an haramta Qungiyar malaman jami’ar watau ASUU. Daga bisani ma aka kori duk malaman jami’o’in Nijeriya. Da malamai suka jajirce a qarshe dai aka daidaita tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU, wannan yarjejeniya ana kiranta da ASUU/FGN Agreement

A sakamakon wannan yarjejeniyar ne aka kafa hukumar taimakon Ilmi ta ETF watau Education Trust Fund. Manufar ETF shi ne tara kuxaxen da za a gudanar da harkokin jami’oi da su. Sai dai ba a samu cimma wannan manufa  ba domin ETF ta zama ta Ilmin Firamare da na Sakandare na da Manyan Makarantun gaba da Sakandire da kuma jami’o’i. ETF ta tara mahaukatan kuxi daga harajin masana’antu da ASUU ta bada shawarar a riqa karva domin Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta da kuxin da za ta biya buqatun jami’o’i. An ci gaba da tara waxannan kuxaxe tun lokacin Babangida har yau. A lokacin mulkin Janar Sani Abacha an qara wani yajin domin gwamnati ta aiwatar ko cika alqawarin da ta yi wa malaman jami’a kamar yadda yake qunshe a cikin yarjejeniyar. Wannan yajin aikin shi ma an yi fiye da watannin shida ana yi, kuma har janar Abacha ya mutu ba a daidaita ba. Mun yi wani yajin lokacin Obasanjo, mun yi lokacin Umaru Musa ‘Yaradua wanda a 2009 aka zauna aka amince aka kuma sa hannu tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU.

Wasu za su ce wai mu ba mu da wata hanyar sa gwamnati ta yi abu ne sai yajin aiki? Amsar ita ce ‘E’ Dalili kuwa shi ne muna da shugabanni ne waxanda ba su san ya kamata ba. Mutane ne waxanda talaka ba ya zuciyarsu, qasar nan bat a gabansu, kuma ba su damu da kowa ba sai abinda zuciyarsu ta raya musu.

Wannan yajin na yanzu da muka tafi ba sabon yajin aiki ba ne. Mun tafi yajin aiki ne bayan mun bi gwamnati iyaka yinmu. Mun lallava ta mun kuma yi ta bada gargaxi cewa matuqar gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da qin aiwatar da abubuwan da aka amince da su a yarjejeniyar da muka qulla da da su to za mu ajiye aiki mu shiga yajin aiki. Gwamnatin Dk. Jonathan ta yi kunnen uwar shegu da mu. Mu ba shegu ba ne to.

Ya kamata jama’a su fahimci cewa ASUU da ‘ya’yanta ba su qaunar yajin aiki ko kaxan domin su ma yana shafar su. Yana shafar aikinsu da xalibansu, suma suna da ‘ya’ya a jami’o’i, saboda haka ana shiga yajin aiki ne kawai bayan an yi iyaka qoqarin abu ya ci tura.

A watan Oktoba na shekarar 2009 Gwamnatin Tarayyar Nijeriya bisa wakilcin jami’anta suka kai matsaya da ASUU aka kuma sa hannu da amincewar ita Gwamnatin Tarayya za ta aiwatar da abubuwan da aka sa hannu a kansu. Manyan abubuwan da aka amince das u sun hada da;

i)                    Samar da kuxaxen da ake buqata domin farfaxo da jami’o’in Nijeriya

ii)                  Taimakon Gwamnatin Tarayya ga Jami’o’in Jihohi

iii)                Qara kasafin kuxi daki-daki har ta kai Nijeriya na ware kashi 26 na kasafin kuxinta ga vangaren ilmi daga 2009 zuwa 2020

iv)                Biyan alawus-alawus na Malamai bisa ayyukan da suka riga suka yi daga 2009-2012.

v)                  Maida shekarun ritaya na Farfesoshi zuwa shekara 70 maimakon shekara 65.

vi)                Miqawa Jami’o’i kadarorin gwamnatin na gine-gine dake Legas domin samar da kuxin tafiyar da jami’o’I kuma a ragewa ita gwamnatin wahala.

vii)              Kafa sashen bincike a kamfanoni domin inganta su maimakon dogaro da qasashen waje koyaushe da kuma samar da kayan aiki a xakunan bincike da ajujuwa a jami’o’i.

Mun tafi yajin aikin gargaxi daga Disamba 8, 2011 zuwa 20 ga Maris 2012 amma abu guda kawai Gwamnatin Tarayya ta aiwatar watau xaga shekarun ritaya zuwa 70. Daga wancan lokacin ASUU ta yi ta faxi tashi da fafutuka ta hanyar tattaunawa da kwamitin aiwatarwa na Gwamnatin Tarayya, tattaunawa da Kwamitin ilmi na Majalisar Tarayya, rubuta wasiqu da bayanai a jaridun duk don gudun shiga yajin aiki. Duk wannan bai yi amfani wurin shawon kan gwamnati tarayya ba.

Daga bisani Gwamnatin Tarayya ta sa kwamiti mai zaman kansa ya zagaya duk jami’o’in qasar nan domin ganin haqiqanin halin da suke ciki, suka kuma kawo mata ruhoto. Ina xaya daga cikin waxanda suka zagaya wasu jami’o’i a gabanshin qasar nan kuma abubuwan da muka gani sun tayar mana da hankali. Lokacin da aka gabatar wa Majalisar gudanarwar Gwamnatin Tarayya da ruhoton sai kunya ta rufe su, kowa ya fara kallon xan uwansa yana cewa shi bai san lalacewar da ta kai haka ba. Wallahi wasu jami’o’in ko darajar Sakandare bas u kai bat a fuskar kayan aiki. Mun ga makarantar da ake lakca a sitadiyom, mun ga wadda malami huxu hard a Farfesa ke zaune a ofishi guda. Mun ga rijiyoyin da xalibai suka faxa saboda neman ruwa. Mun ga xakunan binciken da kayan aikinsu tun na 1960 zuwa 1970 ne, su ake amfani das u. Mun ga… mun ga… abubuwa dai mara sa daxi.

Mu ba jahilai ba ne, kuma kowane xan Nijeriya ya san yadda ake varnar kuxin qasa ta hanyoyi mara sa amfani.  Mun ga yadda ake biyan ‘yan majalisa albashi zabtari-da-kanka (har da masu dumama kujera). Mun ga yadda aka yi da masu satar ragowar kuxin mai wanda har yanzu maganar ta sha ruwa. Mun ga yadda aka sace kuxin NEPA aka yi shiru da maganar. Mun ga yadda ake rabon kuxi ga mutanen da ba sa qarawa qasar nan komai illa wai ana samun mai a yankinsu. Muna ganin yadda gwamnoni ke sayen jiragen sama. Muna ganin varna iri-iri. Duk da wannan sai Ministocin Jonathan su shafawa fuska toka su fito su ce wai Nijeriya ba ta da kuxin da za ta gyara jami’o’i.

Mun ji su xiyansu suna wasu qasashe suna karatu, to amma ai dukiyoyin da suke hannunsu ban a sub a ne na qasa ne, na ‘yan Nijeriya ne. Mu riqo muka ba su. Kuma ba abin kunya ba ne halin da jami’o’i ke ciki a qasar nan. Ba yabon kai ba, malaman da suke koyarwa a jami’o’inmu za su iya koyarwa a kowace qasa a duniya. Amma babu kayan aiki, babu kayan bincike me za ka yi?

Ya kamata mutanen Nijeriya su fahimci cewa zaman da muka yi muna aiki a jami’o’i ba wai don mun rasa aikin yi ba ne, illa kishin qasa. Dukanmu za mu iya barin aji mu shiga gwamnati ko mu shiga siyasa a dama da mu. Za mu iya barin qasar mu tafi ci-rani koma mu yi qaura ta dindindin. To amma, in mun yi haka mun yi wa qasarmu adalci? Mu da kuqin qasa aka ilmantar da mu don haka muka gay a zamar mana wajibi mu zauna mu taimaki qasarmu ta haihuwa.

Lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su fahimci cewa yajin aikin nan da muke yi muna yin shi domin a gyara domin shi kaxai ne yaren da gwamnatocinmu ke ji. Muna neman goyon bayan al’uma da kuma addu’arsu. Allah ya taimake mu a gyara jami’oi’nmu domin qasarmu ta ci gaba amin.

Farfesa Yusuf M. Adamu, marubuci, manazarci, malami ne a sashen labarin Qasa (Geography) na Jami’ar Bayero ta Kano (yusufadamu@gmail.com/www.tagarduniya.blogspot.com)

 

 

  • Locations of visitors to this page

Blog Archive

About Me

My photo
Kano, Kano, Nigeria
Dr. Yusuf M. Adamu, Fulbright Fellow, member, Nigerian Academy of Letters and Fellow of the Association of Nigerian Authors is a Professor of Medical Geography at the Bayero University Kano. He is a bilingual writer, a poet, and writes for children. He is interested in photography and run a photo blog (www.hausa.aminus3.com) All the blogs he run are largely for his hobbies and not his academic interests. Hope you enjoy the blogs.