Tuesday, November 2, 2010

MARUBUTA A AL’UMMA

Kasancewarta makala da aka gabatar a Taron Sanin Makamar Aiki na Marubutan Hausa na Kasa wanda Kungiyar Marubuta ta Nijeriya Reshen Jihar Kano da hadin gwiwar Hukumar Dakunan Karatu ta Jihar Kano suka shirya. Yuli 1st -2nd, 2004 a Dakin Karatu na Murtala Mohammed, Kano.




Wannan take da nake son yin Magana a kansa take ne mai ma’ana a taro irin wannan saboda sa ran da ake yi zai nunawa marubuci ko marubuciya matsayinsa a cikin al’umar da Allah ya halicce shi. Take ne da ake san ran zai fadakar da marubuci ko marubuciya hakkoka da suka rataya a kansu da kuma manufar tasirin abubuwan da suke rubutawa.



Babu al’uma da za ta ci gaba matukar bat a da marubuta. Marubuta sun eke tattara tarihin al’umarsu su adana shi ta hanyar rayayyen adabi. Wasu daga cikinsu ana haihuwarsu ne da baiwar rubutu, wasu kuma kan same ta saboda kokarinsu da kuma dagewa. Duka wadannan rukunai na marubuta bas u iya yin rubutu har sai suna da baiwa ko sun samu baiwa. Amma duka za mu kira sun e marubuta.



Marubuta sun banbanta da sauran mutane ba wai domin sun fi sub a, sai don kawai Allah ya huwace musu wata hanya ta tunani wadda wanda ba marubuci ba, ba shi da ita. Marubuta na yin tunani ne na daban tare da kallon rayuwa da al’amuran da kan je su komo da wata fahimta ta daban. Su kan yi amfani da haruffa zuwa kalmomi da jimloli zuwa shararori domin bayyana tunaninsu wanda zai iya zama tamkar tafsiri ne na rayuwar da suka kalla suke aiki a kan ta.



Marubuci ya banbanta da masanin tarihi domin shi marubucin tarihi na bayyana hakikanin abubuwan da suka faru ne bayan ya tabbatar da afkuwarsu. Masanin tarihi kuma bay a maida hankali a kan kowa da kowa, face wadanada suka yi fice. Saboda haka hanyar da akan bi domin fahimtar yaya al’uma ta rayu a wani zamani shi net a yin nazarin kirkirarrun ayyuka da suka yi a zamaninsu. A nan marubucin zube ko wake ko wasan kwaikwayo kan rubuta wani abu da ya shafi mai mulki da talakansa, mai arziki da mara shi, kyakkyawa da mummuna, mai addini da mara shi, mai azama da malalaci, samari da ‘yan mata, tsofaffi da kananan yara, dabbobi da aljanu da dai sauransu. A cikin irin wadannan ayyuka na adabi ne za a iya fahimtar yadda wani ko wata suka rayu . Misal ga wani wake nan da wani Fir’auna ya rubuta na yabon Ubangiji fiye da shekaru 3000 da suke shude:

Ayyukanka suna da yawa matuka

Ya ubangiji tilo, babu wani tamkar sa

Kai ka hallici duniya yadda ka so

Da kai kadai ne tilo,

Duk mutum, duka dabbobi na gida da na dawa

Duk hallitta mai tafiya bisa dugaduganta

Duk abubuwan dake sama da halittu masu fiffike suna tashi



Kai ka halicci kasashe har da kasar Masar

Ka ajiye kowane mutum a wuri nasa daban

Al’umomi suna harsuna daban daban

Siffarsu ta jiki da launi sun banbanta

Domin ka banbance tsakaninsu.



Daga wannan wake na yabon Ubangiji za mu iya fahimtar yadda Misrawan Dauri a wancan lokaci suka fahimci Ubangiji da yadda tsarin addininsu yake. Ba wannan ne kawai misali ba, akwai misalai da dama da za a iya kawowa daga rubuce-rubucen al’umomi daban daban na duniya. Ko nan in muka dawo gida, za mug a cewa in mun karanta littatafan su Abubakar Imam muka hada su da na su Bashari Farouk Roukbah muka kuma karanta litattafan su Hafsatu AbdulWaheed da na su Ado Ahmad Gidan Dabino, za mu iya bada bayani akan yadda rayuwar Bahaushe ta sauya dangane da al/ada da kuma ma harshe. Idan kana nazarin harshe, babu yadda za a yi ka ga an yi amfani da wasu kalmomi ko an bas u wata ma’ana sai dai-dai zamanin da aka soma hakan. Misali in kana karanta Ruwan Bagaja za ka ga ana amfani ne da famai-famai in ana maganar kudi. Idan ka zo ka na karanta littafi na zamani za ka ga an yi amfani da wata kalma wadda a litattafan baya ba za a bata ma’anar da aka bat a a littafi na yau ba. Alal misali;

“Ka share ta kawai” ko

“Ta na ja masa aji”

Marubuci kan iya jawowa al’umarsa ci aba ko dakushewa kuma matukar ba a fahimci manufar marubuci ba, to ka jahilci fahimtarsa, sai dai kuma shi abu na adabi da zarar marubuci ya fito da shi ya zama mallakar duniya ba tasa ba. Wannan ya sa kowa zai iya fassara rubutu da iya tasa fahimtar wadda ba lallai net a zama ta dace da ainihin abinda shi marubucin ke nufi ba. Babu ja a wannan fuska. A wasu lokuta kuma akan yi dace wurin fadar ainihin manufar marubuci. Ta kowace hanya muka duba dai, rubutu na fita daga ma’anar da marubuci ya ba shi da zarar an fitar da shi. Wannan ya say a zama wajibi marubuci da ke yi wa al’umarsa rubutu ya yi kokarin yi ta yadda manufarsa a ta fito karara kuma a fahimce ita.



Shin wai wanene marubuci? Zai yi matukar wahala a bayyana a bayyane ma’anar ko wanene marubuci. Sai dai wannan ba zai hana mu jarraba bada ma’ana ga kalmar marubuci ba. A tawa fahimta wadda tsukakkiya ce ana iya cewa marubuci mutum wanda kan yi amafani da basirar da Allah ya ba shi ta hanyar kirkirar wani yanani na gasket ko na almara ko wani tunani ko fahimta ta domin gina wasu mutane ko ma’anoni domin isar da wani sako ga al’uma ta zamansa da wadda za ta zo bayansa. MArubuci kan tsara wanann sako nasa ta hanyar mai jan hankali da kuma dadin lafazi tare da cusa kwarewar harshe da yi masa adon da zai sa mai karatunsa ya kusanta da shi ya so shi ya kuma sa mai karatunsa ya rika jin kamar abin da yake karantawa hakika ne. Wannan yana faruwa ne saboda marubuci kan yi amfani da mutane da wurare da ta’adodi da harshe da fahimta irin ta mutanen da ake rubutu dominsu.



Marubuci kan iya yin rubutu domin dalilai masu dama ko wani hali da ya samu kansa ko dai wata manufa. Don haka, marubuci kan iya yin rubutu domin nishadantarwa ko ilmantarwa ko wayar da kai ko farfaganda ko zambo ko neman kudi ko neman suna ko tada zaune tsaye ko yada wata akida da ya yarda da ita ko gina wata manufa ko rusa ta ko domin tabbatar da al’uma a wani tabbataccen ra’ayi. Ko kuma ya yi rubutu wai don rubutu kawai. Marubuci kan yi iyaka kokarinsa wurin shawo kan mai karatu ya yadda ya amince ya kuma hakkake cewa wannan sako nasa gaskiya ne, amintacce ne kuma dauwamamme mai farin jinni.



Wannan ya say a zama wajibi ga al’uma ta dage ta yi tasiri mai kyau ga marubutan da ke cikinta domin yin tasiri ga tunaninsa ta yadda shi kuma zai sarrafa tunaninsa wurin yin rubuce-rubuce da za su dace da al’umarsa su kuma ciyar da ita gaba ba tare da an rika samun tangarda ba. Shi rubutu tamkar kashi ne ko amai, in ka ci zogala sai ka yi kashi bakikkirin in ka ci doya sai ka yi aman kura-kuran doya haka in wake ka ci.



Shi kuma marubuci ya zama lazim ya fahimci cewa zama marubuci al’amari ne babba domin kuwa yana tatatre da hakkoki da nauye-nauye. Na farko marubuci a kodayaushe kokari yake yi ya fahimci al’umarsa. Na biyu duk lokacin da yake tunani dole ne ya rika sanya tunaninsa da mutuntakarsa a ma’auni. A cikin rubutunsa zai iya zama na kwarai ya kuma zama baragurbi, ya zama namiji ya zama mace, ya zama yaro ya zama babbaa da dai sauransu. Wannan na faruwa ne aboda duk lokacin da ya so rubuta wani abu game da wani jinsi ko ajin mutane sai ya yi tunani irin nasu. Abu na uku ba zai san iya tasirin da rubutunsa zai yi ba bayan ya fito da shi. Wannan ya say a zama wajibi marubuci ya tabbatar da cewa al’uma ta tsira daga dafin alkalaminsa ta kuma amfana da rahamar tawwadar alkalaminsa. Duk abinda mutum zai rubuta ya yi tunanin irin tasirin da zai iya jawowa ga al’uma mai kyau ko mara kyau. Wannan ya say a zama dole marubuci musulmi ya yi fancakali da manufar nan ta cewa wai marubuci na da ‘yancin rubuta binda ya ga dama kuma ana yin rubutu ne kawai don rubutu. Ana yin rubutu ne da manufa, kuma ga marubuci musulmi dole ta zama manufa Islamiyya.



Marubuci kan iya zama tamkar dan liken asiri saboda dole sai ya yi bincike mai zurfi akan abinda yake rubutawa in dai har yana so ya rubuta adabi mai rai kuma ingantacce tabbatacce. Idan wani ya gamu da marubuci a wani wuri da yake ganin bai dace ba, zai iya zarginsa da batanci, amma ba lallai bane cewa batanci yaje yi, kila bincike ya je yi. Idan ka ga marubuci a mashaya ko gidan karuwai ko kuwa tare da ‘yan kwaya ko ‘yan daba, bincike na iya kai shi. Da zarar ya fahimci yadda rayuwar wadanda yake so ya yi rubutu a kansu in ya yi maka rubutu sai ka ranstse shi ma dan cikinsu ne. Idan muka karanta littafin Bala Anas Babinlata Sara da Sassaka sai mu rantse Bala ya zauna a Afirka ta Kudu. In ka karanta Karshen Alewa na Marigayi Bature Gagare sai ka ranste tsohon dan tawaye ne, haka in ka karanta ‘Yar Tsana na Ibrahim Sheme sai ka rantse tsohon dan dandi ne. Bincike ne ya bas u wannan dama.



Ta yaya basirar kirkira marubuciya ko marubuciya ke zuwa? Basirar marubuci kan z one ta hanyoyi da dama. Wasu daga zurfin tunani wasu daga karanta ko ganin wani abu wasu kuma daga faruwar wani abu. Ko dai yaya basirar ke zuwa tana samo tushe ne daga al’amuran dan adam na yau da gobe. Gina labarin ko wasan kwaikwayo ko wake kuma kan samu net a hanyar tattara manufar jigon wuri guda tamkar yadda mai zane zanen gine-gine kan yi dan karami. Wasu tun farko su kan san inda labarinsu ko wakensu ya nufa, wasu kuma sai a hankali suke gina shi ta hanyar ba shi kansa labarin dama ya sauya ta yadda al’amura suka kasance. Misali lokacin da na yi tunanin rubuta Idan So Cuta Ne, tun farko na san yadda zan gina labarin da yadda zai kare. Labari ne na wani saurayi da wata budurwa da suka so junansu matukar so amma ba za su yi aure ba, sai dai diyansu za su yi aure. Wannan shine dunkulalliyar manufar Idan So Cuta Ne amma warware jigon ya dauki lokaci. Na dauki lokaci ina ta gina labarin a a kaina ina rubuta wasu abubuwa ina Tarawa. Na dauki lokacin wurin tunanin a wadanne garuruwa zan gina labarin? Su wa da w azan sa a labarin? Wadanne sunaye ne za su dace da kowane tauraro, babba da karami? Yaya ta’ada da salon maganar kowane daga cikinsu za ta kasance da sauransu. Bayan duk na gama wannan aiki na zauna cikin mako guda na rubuta Idan So Cuta Ne.



Wannan ya kawo mu maganar lokacin yin rubutu. Da wane lokaci ake yin rubutu kuma tsawon wane lokaci ya kamata marubuci ya kamata ya dauka kafin y agama wani aji na rubuitu? Ta wannan fuska babu amsa guda daya. Lokacin yin rubutu ya dangantaka ya kuma bambanta daga marubuci zuwa marubuci. Wani kan yi rubutu duk lokacin da ya ga dama, wani sai rubutun ya zo masa don kansa wani kuma kan fara rubutu daga ganin faruwar wani abu ko kuma wani abu ya harzuko shi. Amma dangane da lokaci na rana ko dare, kowane marubuci na da lokacin da yake rubutu. Wasu kuma kan yin me kawai duk lokacin da abin ya zo musu. Dangane da tsawon lokacin da ya kamata a dauka kuwa shi ma ya bambanta da abubuwa da dama. Na farko kaifn basirar marubuci da kwarewarsa. Na biyu sanin abinda zai yi rubutu a kai ciki da waje. Na uku mutuntakarsa, kodai ta zumudi ce ko jirgin dankaro ko kuma madaidaiciya.



A nan ya kamata in yi kira ga al’umarmu da bat a dauki marubuta da muhimanci da da su sauya ra’ayi. A karshe zan iya cewa dan abinda na iya kalatowa kalilan ne daga kalilan dangane da taken wannan makala sai a yi hakuri. Amma zan rufe da tunatar da mu cewa rubutu tamkar shuka ce wanda in hart a girma za ta baka inuwa kuma ka ci ‘ya’yanta. Yana kuma iya zama tamkar dan kunama ko abinda Hausawa ke kira “kaikayi koma kan mashekiya. Rubutu rayyayyen al’amari ne wanda kan wanzu matukar wanzuwar duniya.



Assalamu Alaikum.

2 comments:

Anonymous said...

Haka ta ke! Abin ba dabo ba ne.

Anonymous said...

When ever I put down my pen,to scramble on a piece,be it the never ending tales,or the dancing words. I found my self living in my own little world, where no one or nothing else matters.

  • Locations of visitors to this page

Blog Archive

About Me

My photo
Kano, Kano, Nigeria
Dr. Yusuf M. Adamu, Fulbright Fellow, member, Nigerian Academy of Letters and Fellow of the Association of Nigerian Authors is a Professor of Medical Geography at the Bayero University Kano. He is a bilingual writer, a poet, and writes for children. He is interested in photography and run a photo blog (www.hausa.aminus3.com) All the blogs he run are largely for his hobbies and not his academic interests. Hope you enjoy the blogs.