Dalilan Yajin Aikin ASUU
Koyaushe
a ka ce malaman jami’a na yajin aiki mutane kan faxi albarkacin bakinsu. Wasu
su goyi bayanmu wasu kuma su goyi bayan gwamnati. Wasu kuma su tsaya a
tsaka-tsaki suna ganin laifin kowa. A wannan karo ma haka muka tsincin kanmu.
Da
yawa mutane na mamakin me ya sa muka xauki yajin aiki da muhimmancin da har
wasu suna ganin cewa da mun nemi abu an hana mu sai mu tafi yajin aiki. Wannan
dalili ne ya san a ga ya dace a matsayina na malamin jami’a in yi wa jama’ar
Nijeriya bayani akan halin da muka tsinci kanmu a wannan karo ko ma yi wa juna
adalci.
Yajin
aikin Malaman Jami’a da ya fara shahara shi ne wanda aka yi lokacin mulkin soja
na Janar Babangida qarqashin shugabanci Dk. Attahiru Jega a 1992. Yajin aiki ne
da aka yi fiye da wata shida ana yi har ya jawo an rufe dukkan jami’o’in
Nijeriya. A wannan lokacin, bayan tsayar da albashin malamai da aka yi har ma
ta kai an haramta Qungiyar malaman jami’ar watau ASUU. Daga bisani ma aka kori
duk malaman jami’o’in Nijeriya. Da malamai suka jajirce a qarshe dai aka
daidaita tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU, wannan yarjejeniya ana kiranta da ASUU/FGN Agreement
A
sakamakon wannan yarjejeniyar ne aka kafa hukumar taimakon Ilmi ta ETF watau Education Trust Fund. Manufar ETF shi ne
tara kuxaxen da za a gudanar da harkokin jami’oi da su. Sai dai ba a samu cimma
wannan manufa ba domin ETF ta zama ta
Ilmin Firamare da na Sakandare na da Manyan Makarantun gaba da Sakandire da
kuma jami’o’i. ETF ta tara mahaukatan kuxi daga harajin masana’antu da ASUU ta
bada shawarar a riqa karva domin Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta da kuxin da za
ta biya buqatun jami’o’i. An ci gaba da tara waxannan kuxaxe tun lokacin
Babangida har yau. A lokacin mulkin Janar Sani Abacha an qara wani yajin domin
gwamnati ta aiwatar ko cika alqawarin da ta yi wa malaman jami’a kamar yadda
yake qunshe a cikin yarjejeniyar. Wannan yajin aikin shi ma an yi fiye da
watannin shida ana yi, kuma har janar Abacha ya mutu ba a daidaita ba. Mun yi
wani yajin lokacin Obasanjo, mun yi lokacin Umaru Musa ‘Yaradua wanda a 2009
aka zauna aka amince aka kuma sa hannu tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU.
Wasu
za su ce wai mu ba mu da wata hanyar sa gwamnati ta yi abu ne sai yajin aiki?
Amsar ita ce ‘E’ Dalili kuwa shi ne muna da shugabanni ne waxanda ba su san ya
kamata ba. Mutane ne waxanda talaka ba ya zuciyarsu, qasar nan bat a gabansu,
kuma ba su damu da kowa ba sai abinda zuciyarsu ta raya musu.
Wannan
yajin na yanzu da muka tafi ba sabon yajin aiki ba ne. Mun tafi yajin aiki ne
bayan mun bi gwamnati iyaka yinmu. Mun lallava ta mun kuma yi ta bada gargaxi
cewa matuqar gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da qin aiwatar da abubuwan da aka amince
da su a yarjejeniyar da muka qulla da da su to za mu ajiye aiki mu shiga yajin
aiki. Gwamnatin Dk. Jonathan ta yi kunnen uwar shegu da mu. Mu ba shegu ba ne
to.
Ya
kamata jama’a su fahimci cewa ASUU da ‘ya’yanta ba su qaunar yajin aiki ko
kaxan domin su ma yana shafar su. Yana shafar aikinsu da xalibansu, suma suna
da ‘ya’ya a jami’o’i, saboda haka ana shiga yajin aiki ne kawai bayan an yi
iyaka qoqarin abu ya ci tura.
A
watan Oktoba na shekarar 2009 Gwamnatin Tarayyar Nijeriya bisa wakilcin
jami’anta suka kai matsaya da ASUU aka kuma sa hannu da amincewar ita Gwamnatin
Tarayya za ta aiwatar da abubuwan da aka sa hannu a kansu. Manyan abubuwan da
aka amince das u sun hada da;
i)
Samar da kuxaxen da ake buqata domin
farfaxo da jami’o’in Nijeriya
ii)
Taimakon Gwamnatin Tarayya ga Jami’o’in
Jihohi
iii)
Qara kasafin kuxi daki-daki har ta kai
Nijeriya na ware kashi 26 na kasafin kuxinta ga vangaren ilmi daga 2009 zuwa
2020
iv)
Biyan alawus-alawus na Malamai bisa
ayyukan da suka riga suka yi daga 2009-2012.
v)
Maida shekarun ritaya na Farfesoshi zuwa
shekara 70 maimakon shekara 65.
vi)
Miqawa Jami’o’i kadarorin gwamnatin na
gine-gine dake Legas domin samar da kuxin tafiyar da jami’o’I kuma a ragewa ita
gwamnatin wahala.
vii)
Kafa sashen bincike a kamfanoni domin
inganta su maimakon dogaro da qasashen waje koyaushe da kuma samar da kayan
aiki a xakunan bincike da ajujuwa a jami’o’i.
Mun
tafi yajin aikin gargaxi daga Disamba 8, 2011 zuwa 20 ga Maris 2012 amma abu
guda kawai Gwamnatin Tarayya ta aiwatar watau xaga shekarun ritaya zuwa 70.
Daga wancan lokacin ASUU ta yi ta faxi tashi da fafutuka ta hanyar tattaunawa
da kwamitin aiwatarwa na Gwamnatin Tarayya, tattaunawa da Kwamitin ilmi na
Majalisar Tarayya, rubuta wasiqu da bayanai a jaridun duk don gudun shiga yajin
aiki. Duk wannan bai yi amfani wurin shawon kan gwamnati tarayya ba.
Daga
bisani Gwamnatin Tarayya ta sa kwamiti mai zaman kansa ya zagaya duk jami’o’in
qasar nan domin ganin haqiqanin halin da suke ciki, suka kuma kawo mata ruhoto.
Ina xaya daga cikin waxanda suka zagaya wasu jami’o’i a gabanshin qasar nan
kuma abubuwan da muka gani sun tayar mana da hankali. Lokacin da aka gabatar wa
Majalisar gudanarwar Gwamnatin Tarayya da ruhoton sai kunya ta rufe su, kowa ya
fara kallon xan uwansa yana cewa shi bai san lalacewar da ta kai haka ba.
Wallahi wasu jami’o’in ko darajar Sakandare bas u kai bat a fuskar kayan aiki.
Mun ga makarantar da ake lakca a sitadiyom, mun ga wadda malami huxu hard a
Farfesa ke zaune a ofishi guda. Mun ga rijiyoyin da xalibai suka faxa saboda
neman ruwa. Mun ga xakunan binciken da kayan aikinsu tun na 1960 zuwa 1970 ne, su
ake amfani das u. Mun ga… mun ga… abubuwa dai mara sa daxi.
Mu
ba jahilai ba ne, kuma kowane xan Nijeriya ya san yadda ake varnar kuxin qasa
ta hanyoyi mara sa amfani. Mun ga yadda
ake biyan ‘yan majalisa albashi zabtari-da-kanka (har da masu dumama kujera).
Mun ga yadda aka yi da masu satar ragowar kuxin mai wanda har yanzu maganar ta
sha ruwa. Mun ga yadda aka sace kuxin NEPA aka yi shiru da maganar. Mun ga yadda
ake rabon kuxi ga mutanen da ba sa qarawa qasar nan komai illa wai ana samun
mai a yankinsu. Muna ganin yadda gwamnoni ke sayen jiragen sama. Muna ganin
varna iri-iri. Duk da wannan sai Ministocin Jonathan su shafawa fuska toka su fito
su ce wai Nijeriya ba ta da kuxin da za ta gyara jami’o’i.
Mun
ji su xiyansu suna wasu qasashe suna karatu, to amma ai dukiyoyin da suke
hannunsu ban a sub a ne na qasa ne, na ‘yan Nijeriya ne. Mu riqo muka ba su.
Kuma ba abin kunya ba ne halin da jami’o’i ke ciki a qasar nan. Ba yabon kai
ba, malaman da suke koyarwa a jami’o’inmu za su iya koyarwa a kowace qasa a
duniya. Amma babu kayan aiki, babu kayan bincike me za ka yi?
Ya
kamata mutanen Nijeriya su fahimci cewa zaman da muka yi muna aiki a jami’o’i
ba wai don mun rasa aikin yi ba ne, illa kishin qasa. Dukanmu za mu iya barin
aji mu shiga gwamnati ko mu shiga siyasa a dama da mu. Za mu iya barin qasar mu
tafi ci-rani koma mu yi qaura ta dindindin. To amma, in mun yi haka mun yi wa
qasarmu adalci? Mu da kuqin qasa aka ilmantar da mu don haka muka gay a zamar
mana wajibi mu zauna mu taimaki qasarmu ta haihuwa.
Lokaci
ya yi da ‘yan Nijeriya za su fahimci cewa yajin aikin nan da muke yi muna yin
shi domin a gyara domin shi kaxai ne yaren da gwamnatocinmu ke ji. Muna neman
goyon bayan al’uma da kuma addu’arsu. Allah ya taimake mu a gyara jami’oi’nmu
domin qasarmu ta ci gaba amin.
Farfesa
Yusuf M. Adamu, marubuci, manazarci, malami ne a sashen labarin Qasa
(Geography) na Jami’ar Bayero ta Kano (yusufadamu@gmail.com/www.tagarduniya.blogspot.com)
No comments:
Post a Comment