Daga
Dr Yusuf Adamu
yusufadamu2000@yahoo.com
Cibiyar Nazarin Al’adun Hausawa
Da kuma
Jami’ar Bayero ta Kano
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai. Tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen talikai kuma abin koyi, Muhammadu da alayensa da sahabbansa da kuma masu bin tafarkinsa.
Da farko zan fara da neman afuwa saboda an sani yin abinda ya fi karfina. Mai girma Dan Masanin Kano ne ya kamata ya gabatar da wannan jawabi da irin hikimarsa da kwarewarsa a harshe ta balaga da kuma dadadan kalamansa. Allah bai ba shi damar halarta ba.
Lokacin da aka nemi in yi wannan jawabi (shekaranjiya kenan) na so in ce ba zan iya ba domin kuwa ba zan iya taka sawun Dan Masani ba, ba kuma zan iya yin irin tasa ba. Amma dalilai biyu sun san a amince, na farko dai Uban Cibiyar Nazarin Al’adun Hausawa (wadda ni darakta ne a cikinta) watau Dr Magaji Dambatta da kuma shugaban wannan Cibiya Farfesa Abdalla Uba Adamu ne suka tuntube ni akan maganar, su kuma mutane ne da ba zan iya ce musu a’a ba. Na biyu kuma ganin irin gudunmuwar da Ali Kwara ke bayar wa ta sa na ga bai dace abinsa ya taso ba ace ban bada gudunmuwa ba. Saboda haka sai ayi hakuri da dan abinda zan iya fada a wannan taro mai albarka.
Manyan baki, kowa ya sani cewa Ma’aiki mai tsira da aminci ya ce in musulmi ya ga wani abu na laifi na faruwa a al’uma to ya gyara ba hannunsa, in ba zai iya ba ya gyara da bakinsa, in kuma ba zai iya ba to ya ki abin a zuciyarsa. Wannan hadisi ya takaita mana rawar da Ali Kwara ke takawa a fuskar tsaro a wannan kasa.
Babu shakka, matsalar tsaro da yi tsamari a wannan kasa tamu, dalilai na talauci da hadama da rashin dangana da zalunci da rashin kulawar shugabanni da sauran dalilai sun sa yau dan Nijeriya ba shi da tsaro a duk inda yake. In yana zaune gida cikin iyalinsa ba shi da kwanciyar hankali, in yana hanya zai tafi aiki ko kasuwanci ba shi da kwanciyar hankali, in yana ofis ko wurin sana’arsa ba shi da kwanciyar hankali. In ya zauna a cikin talauci ba shi da kwanciyar hankali, in kuma ya nemi arziki ba shi da kwanciyar hankali. Wannan na faruwa ne duk da cewa akwai hukumar ‘yan sanda a kasa.
Babu yadda za a yi al’uma ta ci gaba matukar babu tsaro, tsaro kuwa ba zai samu ba har sai hukumomin da suke da hakkin tabbatar da shi sun yi aikin da ya dace kuma al’uma ta taimakawa hukuma. In mun koma tarihi za mu ga yadda aka tabbatar da tsaro a Daular Sakkwato ta yadda har mace za ta iya daukar kwando cike da zinari daga bangare guda na daular zuwa wani, misali daga Sakkwato zuwa Kano ita kadai ba tare da wani abu ya same ta ba. Kuma in mun koma tsawon tarihi za mu ga yadda Sayyidina Umar Dan Haddabi (Allah ya yarda da shi) ya inganta tsaro ta yadda kowa a daular Muslunci ya zauna lafiya kuma addini ya yadu.
Kodayake wannan ba lokaci ne da zamu kawo laifuffukan hukuma ba, ya kamata a fahimci cewa harkar tsaro ba abin wasa ba ce, kuma babu yadda za a yi a samu tsaro a kowace irin kasa wadda shugabanninta ba su da adalci, talakawanta ba su da dangana, kuma hukumonin tsaron su ba su da alkibla. Wannan hali da muke ciki ya kamata a sauya shi matukar ana so a zauna lafiya, kuma hakkin kowane dan kasa ne ya bada gudunmuwarsa dai dai hali.
Hukumar ‘yansanda wadda hakkin kare rayuwa da mutunci da dukiyoyin jama’a ke hannunta ba ta da halin yin aikin da ake nema ta yi, kuma ba za ta iya yi ita kadai ba. Jama’a da dama sun sani cewa ‘yan sanda ba su da cikakkun kayan aiki, ba a biyan su albashin da ya dace kuma a lokacin da ya dace, sannan mafi yawancin jama’ar gari ba sa taimakawa hukuma ta hanyar sanar da ita bayanai akan masu laifuffuka saboda tsoron abinda ka je ya komo.
A cikin irin wannan hali ne Allah ya kawo Ali Kwara wanda ga abinda muka sani dan kasuwa ne amma ya koma mafaraucin masu laifi. A wanann fim da aka kira ALI KWARA, an yi kokarin a bada tarihinsa ne a fakaice, ma’ana masu shirya fim din sun yi kokarin tunatar da jama’a halin da ake ciki na rashin tsaro da kuma hanyoyin da ‘yan fashi ke bi suna yi wa mutane fashi da kuma rawar da shi Ali Kwara ke takawa.
Na tabbatta daga cikin manufofin ‘yin wannan fin sun hada da yabawa shi wannan bawan Allah da kuma jawo hankalin al’uma ga ayyukansa na alheri ta yadda kila za a iya yi wa wasu sassa na al’uma allura ko suma za su yi koyi da shi.
Fim din ya yi kokarin nuna abubuwa kamar haka:
i) Mafakar ‘yan fashi da makami
ii) Hanyoyin da suke bi don neman bayani akan mutanen da za su yi wa fashi.
iii) Ire-iren mutanen dake yin fashi da dalilansu, misali a fim din an nuna gungu har 7 na ‘yan fashi, daga masu amfani da bindigogin gargajiya, zuwa masu amfani da manyan bindigogi na zamani har ma da masu amfani da cinyar kaza don ci da buguzum.
iv) Ya nuna mana yadda ‘yan fashi ke rayuwarsu da yadda suke kasha kudadensu.
v) Ya nuna mana yadda ma ake yin fashi ko a gidajen mutane ko a hanya ko a ofis.
vi) Ya nuna mana yadda mata ma suke shiga harkar fashi da makami
vii) Da kuma yadda Ali Kwara ke gudanar da ayyukansa tare da hadin kan hukuma ‘yan sanda ta kasa.
Babban abinda ya kamata mu fahimta daga fim din shi ne kusan duk satar da za a yi ana yinta ne bayan ‘yan fashin ko abokan harkarsu sun tattara musu bayanai sun sanar da su. Kuma ya nuna mana muhimmancin sirri musamman a wannan lokaci na wayar salula. Yadda mutanen ke sakin baki suna maganar dukiya a bainar jama’a na iya sa su a hatsari babba.
Duk da cewa akwai kura-kurai ga yadda aka shirya wannan fim (wanda a shirye muke mu ba masu fim din shawara ta yadda za su inganta shi) lallai ne a yaba musu matuka bisa kokarin da suka yin a shirya wannan fim. Babu shakka, wannan wani salo ne da zai inganta sana’ar fim domin za ta bada damar masu fina-finai su fara shirya fina-finai akan mutanen kirki abin koyi ga al’uma. Ina fatan mahalarta wannan taro na yau za su ba su gudunmuwa sosai domin a kara musu kwarin gwiwa.
Ya kamata a wannan gaba in yi kira ga Mai martaba Sarkin Kano Alhaji (Dr) Ado Bayero CFR da kuma Gwamnatin Jihar Kano da su yi kokari su dawo da tsarin nan da ya ba dagatai da masu unguwanni hurumi da kuma damar tattara da adana bayanai akan mutanen da ke zaune a unguwanninsu da abubuwan da ke faruwa, su kuma rika sanar da hukumomin tsaro akai-akai. Babu yadda za a yi a tabbatar da tsaro har sai an hada da shugabanninmu Sarakuna, duk wanda ya ratso inda aka fito ko kuma ya karanta tarihi ya san irin rawar da masarautu suka taka wurin kyautata tsaro a baya.
A karshe ina godiya saboda saurare na da aka yi, ina kuma rokon Allah ya maida kowa gida lafiya, ya kuma kawo mana sauyi mafi alheri a wannan kasa tamu. Shi kuma Ali Kwara, Allah ya karfafe shi ya kuma tsare shi amin.
Bissalam.
July 21, 2007
An gabatar da wannan jawabi a bikin kaddamar da Fim mai suna ALI KWARA wanda aka yi a Sani Abacha Indoor Stadium a Birnin Kano, ranar 21/7/2007.
This blog contains some of my writings of general nature. They are mainly my views on so many things. Enjoy
Thursday, July 26, 2007
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Blog Archive
- March (1)
- August (2)
- January (1)
- April (1)
- October (1)
- March (2)
- January (2)
- October (1)
- August (1)
- September (1)
- June (1)
- March (1)
- November (1)
- June (2)
- May (1)
- April (1)
- December (1)
- October (1)
- July (2)
- June (1)
- May (1)
- March (1)
- January (2)
- October (1)
- September (2)
- August (4)
- July (1)
- March (1)
- February (2)
- December (4)
- July (1)
- June (3)
About Me
- Yusuf M. Adamu
- Kano, Kano, Nigeria
- Dr. Yusuf M. Adamu, Fulbright Fellow, member, Nigerian Academy of Letters and Fellow of the Association of Nigerian Authors is a Professor of Medical Geography at the Bayero University Kano. He is a bilingual writer, a poet, and writes for children. He is interested in photography and run a photo blog (www.hausa.aminus3.com) All the blogs he run are largely for his hobbies and not his academic interests. Hope you enjoy the blogs.
No comments:
Post a Comment