Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
Allah ka jikan Bashari Farouk Roukbah. Lokacin da na samu labarin rasuwar malam Bashari ina Gusau, akan hanyata ta zuwa aikin Hajjin bana. Na yi bakin ciki matuka musamman ma da yake bai fi mako guda ba nake tunanin ya kamata in je in gaishe shi. Allah bai yi za mu sake saduwa ba, saduwarmu ta karshe a Giginyu ne lokacin da ya zo ta'aziyyar rasuwar mahaifin nasiru Mudi Giginyu watanni biyu da rabi da suka wuce, mun jima muna tattaunawa kamar koyaushe akan harkar rubutu, bayan ya yi addu'a.
Na fara haduwa da Malam bashari a 1985, na gama makarantar Sakandare na dawo gioda ina jiran fitowar WAEC, sai wani aminin mahaifina da ake kira Malam Yusha'u Dutse ya cewa babana zai hada ni da wani abokinsa marubuci kuma mawallafi tunda ya ga ina da sha'awar rubuce-rubuce, ile kuwa muka je ya kai ni gidansa. Tun ganina na farko da shi na fahimci cewa lallai wannan bawan Allah ya yi mun kama da marubuci, a shekarun da suka biyo baya muka saba da shi matuka. Mun kafa wata Kungiya ta marubuta mai suna Kungiyar Matasa Marubuta a 1986-87, muka kuma nemi su biyun su zamar mana iyayen Kungiya, daga baya muka kara da hajiya Hafsatu Abdulwahid.
Lokacin ina karatu a Jami'ar Usmanu Danfodiyo na na sa an gayyaci Bashari sau uku a Jami'ar, zuwa na farko da na biyu ya gabatar da makalu enakan adabi, zuwa na uku kuma a 1990 ya gabatar da makala akan Jangwarzon Shugaban Kasa: Janar Murtala Mohammed. Lokaci da na tafi hidimar Kasa a Dutsin Ma, na sake gayyatarsa ya yi wa dalibaina lakca kan RUwayen Gujjiyar Jiki (Hormones) daga nan kuma da muka fara harkar ANA muka shigo da shi a matsayin uban kungiya. Roukbah ya halarci tarurrukanmu da yawa, kuma da dama a cikinmarubutan Hausa sun san shi.
Ya rubuta litattafai fiye da arba'in, amma kadan aka buga cikinsu akwai Matar Mutum Kabarinsa, Hantsi Leka Gidan Kowa, Abinda ka shuka, Aikin Hajji na I-III, da wasu litattafan yara. Ya fara buga mujallar Abokiyar Hira da kuma Jakadiyar Muslunci. Akwai kuma littatafansa da dama wadanda ba a buga ba, wasu mun sansu mun kuma gansu, wasu kuma ba mu gansu ba ko ba mu sansu ba, cikinsu har da Mutum Dan Nuhu Jikan Adam.
Malam Basjari, shi ne mutum na farko da ya fara sanar da mu abinda ake nufi da wallafa (Publishing) , da kuma warware mana ma'anar hakkin mallaka (copyright), mun kuma karu matuka daga irin basirar da Allah ya bashi. Mu biyar muka yi yayin zuwa gidansa akai-akai sauran sune Nasiru Mudi Giginyu (Wanda muke ganin ya juye ya zama Roukbah a tunani) da Lawan Adamu (Kaifa) daga baya kuma akwai Baba Ali Abubakar (Dama Hannun Agogo zai dawo baya) da kuma Jibrin Ali Giginyu tsohon editan Sunday Truimph. Duk sanda muka je, bayan mun tatattauna akan rubutu, mu kan kuma tattauana akan rayuwar yau da kullum da kuma siyasar Nijeriya da kuma ta jihar Kano kai har ma da ta sarauta (tunda shi jikan Abdullahi Bayero Bayero ne).
Muna fatan iyalansa za su tattara rubuce-rubucensa domin adana su muna kuma fatan ANA da suaran mutane masoya adabi za su yi kokarin buga sauran litatttafansa da ba buga ba. Lallai ne mu raya sunansa. Babu shakka, marubuta, da manazarata da mawallafa da kuma dukan al'umar Musulmi mun yi rashin wannan bawan Allah ya kuma kyautata bayansa amin. Babbar addu'armu kenen.
Allah ya jikanka Bashari, mu kuma in lokacinmu ya zo, Allah ka amshi rayukanmu muna masu imani.
This blog contains some of my writings of general nature. They are mainly my views on so many things. Enjoy
Sunday, December 9, 2007
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Blog Archive
- December (1)
- March (1)
- August (2)
- January (1)
- April (1)
- October (1)
- March (2)
- January (2)
- October (1)
- August (1)
- September (1)
- June (1)
- March (1)
- November (1)
- June (2)
- May (1)
- April (1)
- December (1)
- October (1)
- July (2)
- June (1)
- May (1)
- March (1)
- January (2)
- October (1)
- September (2)
- August (4)
- July (1)
- March (1)
- February (2)
- December (4)
- July (1)
- June (3)
About Me
- Yusuf M. Adamu
- Kano, Kano, Nigeria
- Dr. Yusuf M. Adamu, Fulbright Fellow, member, Nigerian Academy of Letters and Fellow of the Association of Nigerian Authors is a Professor of Medical Geography at the Bayero University Kano. He is a bilingual writer, a poet, and writes for children. He is interested in photography and run a photo blog (www.hausa.aminus3.com) All the blogs he run are largely for his hobbies and not his academic interests. Hope you enjoy the blogs.
1 comment:
asslam alaikum
gaisuwa da fatan alkhairi ga doctor bisa wannan maqala da ya karemu da ita,
babu shakka mutane dayawa suna bukatar sanin abubuwa dayawa bisa kayinsu da rayuwarsu da kasarsu da addininsu da al'adunsu
al'ummomi dayawa sunyi rubuce rubuce da yarukansu, kuma sunata yi amma mutanenmu yan nigeria, galiban suna rubutu ne da yaren turawan mulkin mallaka
musamman manyan malaman jam'iaat namu,
ina fatan doctor ze cigaba da rubuto mana irin wadannan maqalat dawaninsu da hausa ko fulfulde, domin musan kanmu mu tattauna matsalolin a sirrance tsakaninmu ,kuma mu samu maganin cutattukan da suka hana ksarmu da mutanenmu ci gaba
nagode
ALLAH ya taimaka ya kuma saka da lakhairi
Post a Comment