Friday, February 15, 2008

FIR'AUNONIN MASAR TA DAURI

Na gabatar da wannan makala a bikin bikin Makon Hausa na Jami'ar Bayero ta Kano ranar, 11/9/2000
GABATARWA
An nemi in gabatar da makala akan Fir’aunonin Masar ta Dauri. Wannan a gaskiya ba karamin aiki ne a gare ni ba. Na farko dai wannan abu ne da ya shafi tarihin wayewar kai mafi tsawo da dadewa a duniya. Ita kuwa Masar ta Dauri gidan tarihi ce. In aka ce za yi lakca akan Masar ta dauri a kullum, za shekara guda ba a kare ba. Don haka, kada a yi tsammani zan iya yin bayani da zai zama mai gamsarwa game da Fir’aunonin Masar ta dauri, zan dai tsakura kadan daga kalilan da na sani game da taken jawabina na yau. Kafin mu shiga harkar bayani akan Fir’aunoni bari mu fara da yin sharar fage akan wasu ‘yan bayanai da suka shafi ita Daular /Daulolin Masar ta Dauri dangane da tarihinta, tsarin rayuwa da addini.

MASAR KYAUTAR NILU
Kufakar kogin Nilu (Nile Valley) na daya daga cikin wurare na farko na wayewar kan dan adam. Masani Herodotus dan kasar Girka, tun lokaci mai tsawo ya kira Masar a matsayin kyautar kogin Nilu saboda dalilai kamar haka; kogin Nilu ne mafi girma a kogunan duniya, tsawonsa ya kai kilomita 6671. Ya taso ne daga tafkin Victoria ya malalo ta Uganda ya biyo ta Sudan sannan ya shigo kasar Masar ya malala ya fada tekun Mediterranean. Idan an dubi Masar za a lura cewa kusan dukanta hamada ne ba don kogin Nilu da ya ratsa ta cikinta ba. Ratsawar kogin Nilu ne ya sa kufadar kogin ta zama mai matukar ni’ima ta fuskar shuke-shuke da noman rani. Duk shekara, mutanen wannan wuri kan dogara ne ga turbaya mai taki da kogin kan amayar ta hanyar yin ambaliya ta yadda bangarorin kogin biyu za su wadatu da taki domin yin noman rani da na damina. Ta haka mazauna wurin ke samun wadatuwar abinci har ma su sayar ga wasu kasashe. Wannan damar ce ta bada samuwar wayewar kai a wurin tun lokaci mai tsawon gaske.

ADDININ MISRAWAN DAURI
Misrawan dauri mutane ne masu addini. Ma’ana suna bin dokokin addinsu sau da kafa. Sai dai su ba mutane masu bautawa Ubangiji guda ba. Suna da iyayen giji da dama, duk da cewa suna daukar shi kansa Fir’auan a matsayin Ubangiji. A kowane babban birni akwai mabautu. Kowane birni na da ubangijinsa, haka kauyuka da gidaje, sai dai akwai ubangijin da kowa yake bi. Wasu daga cikin Iyayen gijin Misrawan dauri sun hada da;
Amun-Ra Ubangiji-Rana
Osiris Ubangijin Matattu
Isis Matar Osiris
Horus [an Osiris
Anubis Ubangijin Jana’iza
Ma’at Uwargijiyar Gaskiya
Thoth Ubangijin Rubutu
Sekhmet Uwargijiyar Yaki.
Ptah Ubangijin Halitta
Mut Uwargijiyar Sama’u kuma uwar Fir’auna
Tunda suna bautar Iyayen giji ne da dama, a wasu lokuta wasu Iyayen giji suna zama muhimmai fiye da wasu. Alal misali Amun ko Amon karamin Ubangiji ne, sai a sabuwar masarauta, bayan an dawo da babban birnin daular Thebes sannan ya zamo muhimmin ubangiji. Lokacin babban birnin yana Memphis babban ubangijin Misrawa a lokacin shi ne Ptah.

MUTUWA DA HISABI
“Jinjina a gareka Ubangijina Osiris! Zan tsira da gangar jikina har abada. Ba zan rube ba, ba zan zama abincin tsutsotsi ba; Ina tabbace, Ina raye, Ina da kuzari na, na tashi cikin salama, kayan cikina ba su rube ba, idanuwa na ba su lalace ba, ba a raba kaina da wuyana ba, gangar jikina za ta tabbata, ba za ta shude ba” Wannan wani bayani ne na karanto maku daga cikin Littafin Matattun (Book of the dead) daya daga cikin manyan bayanan da Masar ta dauri ta bar mana na dangane da yadda Misrawa suka dauki mutuwa. Masu ilmin kufai sun gano cewa a cikin kowane kabari, akwai wasu rubuce-rubuce da ake yi, wadanda manufarsu ita ce ta taimakawa mamaci ya isa lahira cikin nasara. Shi wannan ba saukaken littafi ba ne, a ainihin gaskiya ma masani Lepsius ne ya sawa tattararrun bayanan littafin matattu wanda ya buga a 1842.

Misrawan dauri sun yadda cewa in an mutu za a yi wa mamaci hisabi. Misali, in mutum ya mutu ana kyankyame gawarsa ne domin ya ji dadin yin sabuwar rayuwar lahira. To, bayan an yi bayanan nan na rubutu a kabarinsa wanda ake ganin kamar shine fasfon tafiya, sai kuma a kai ruhin mutum wurin da zai yi bayanin ayyukan da ya yi a rayuwar duniya. Misali mutum zai yi bayani kamar haka “ban tauye ma’auni ba, ban hana jariri shan mama ba, ban karkatar da hanyar ruwa ba, ban tauye hakkin maraya ba, ban kashe kowa ba..” da sauransu. Daga nan sai a dauko zuciyar mamaci a sa ta a sikeli. A hannu guda na sikelin kuma sai a sanya gashin kaza ko na agwawa ko wani tsuntsu a auna. Idan gashin ya rinjayi zuciyar mutum, to ya haye kenan, in kuwa zuciyar mutum ta rinjayi gashin nan to mutum ya kade har ganyensa kenan.

SARAUTAR FIR’AUNA
Da farko ya dace mu gano asalin kalmar Fir’auna. Daga ina ta samo asali, kuma me take nufi. To ita dai kalmar Fir’auna ta samo tushe ne daga harshen Misrawan dauri. Ita dai kalmar Fir’auna da (Ingilishi Pharaoh) tana nufin ‘babban gida’ da harshen Misrancin Dauri. A dauri ana amfani da kalmar ne domin bayyan fadar Mai sarautar Misrawa. An fara amfani da kalmar ne domin kiran Masu Sarauta daga wajajen 1400BC. Ta kokarin kiran dan sarauta dan babban gida shi ne har kalmar ta juye ta zama taken sarauta. A tsarin addininsu, Fir’auna an dauke shi a matsayin dan Osiris, daya daga cikin Iyayen gijinsu. Yana mulki ne a duniya a matsayin wakilin Osiris da sauran iyayen gijin Misrawa. Saboda haka, shi ne shugaban addini da kuma mayaka. A wasu lokuta ma ana daukar Fir’auna a matsayin wani dan karamin ubangiji tunda shi wakilin Osiris ne. Daga cikin fitattun Fir’aunonin da aka yi sun hada da Khufu da Zoser (Djoser) da Thutmose I da Thutmose II da Akhanaten da Ramses II, da kuma Fir’auniya Hatshepsut. Za mu yi bayani akan wasu daga cikin wadannan Fir’aunoni.
Mai Sarauta na farko da za a iya cewa shi ne ya kafa daular Masar ta Dauri shi ne Menes ko Nermer. Shi Menes shi ne ya hade garuruwan dake Kudancin kufadar kogin Nilu da kuma na Arewacin kogin Nilu. Ga jerin Gidajen Sarauta da kuma sunayen wasu daga cikin Fir’aunonin da aka yi a Masar daga gabanin samuwar Masarautu zuwa zamanin Girkawa da Rumawa.
ZAMANIN MULKIN FIR’AUNONIN MASAR
Kafin samuwar Masarautu Kafin 3150 BC
Masaurautun farko-farko 3150BC-2686BC Gidajen Sarauta I -2
Tsohuwar Masarauta 2686-2181BC Gidajen Sarauta 3 - 6
Tsaka-tsaki na farko 2181-2040BC Gidajen Sarauta 6 – 11
Masarauta ta Tsakiya 2040-1782BC Gidajen Sarauta 11-13
Tsaka-tsaki na biyu 1782-1570BC Gidajen Sarauta 13-17
Sabuwar Masarauta 1570-1070BC Gidajen Sarauta 18-20
1570-1293BC Gidajen Sarauta 28
1570-1546 Ahmose
1551-1524 Amenophis I
1524-1518 Tuthmosis I
1518-1504 Tuthmosis II
1504-1450 Tuthmosis III
1498-1483 Hatshepsut
1453-1419 Amenophis II
1419-1386 Tuthmosis IV
1386-1349 Amenophis III
1350-1334 Amenophis IV(Akhanaten)
1336-1334 Smenkhkare
1334-1325 Tutankhamun
1325-1321 Ay
1321-1293 Horemheb
1293-1185 Gidan Sarauta na 21
1293-1291 Ramesses I
1291-1278 Seti I
1279-1212 Ramesses II
1235-1224 Merneptah
1185-1070 Gidan Sarauta na 20
1182-1151 Ramesses III
Tsaka-tsaki na uku 1070-664BC Gidajen Sarauta na 21-25
Masarautun karshe-karshe 664-332 BC Gidajen Sarauta na 26-31
Zamanin Girkawa-Rumawa 332BC-395AD Gidajen Sarauta na 26-31
(Sarakunan Talamawa –Ptelemies da na Rum)

FIR’AUNA KHUFU DA ZOSER
Yanzu kuma sai gabatar da bayani akan wasu daga cikin wadannan Fir’aunoni da suka gabata. Dole ne mu ambaci Fir’auna Khufu da Zoser koda a gurguje ne domin kuwa sune suka gina Dalar Dutse da aka ce yana daga cikin manyan abubuwan mamaki na duniyar dauri guda bakwai. Wadannan Fir’aunoni na farko sune suka gina manyan abubuwan tarihi da har yanzu muke takama da su a matsayin kayan tarihi. Dalar Dutse da Mutum-Zaki (Sphinx) abubuwa ne na ban al’ajabi. Misali Dalar-Dutsen da suka gina takai kafa479 a tsawo, ta kunshi a kalla bulo (wanda kowane ya kai ton 2) guda 2,300,000. Herodotus, masanin Labarin {asa da Tarihi dan kasar Girka ya ruwaito cewa, sai da mutane 100,000 suka yi shekaru ashirin suna gina shi. Tirkashi, har yanzu abin da daure kai, domin an kasa gano yadda aka gina su. Shi kuma Mutum-Zaki (watau Sphinx) ya kai kafa 66 a tsaye, tsawonsa kafa 189.
Zanen Dutse mai nuna Khufu na karya makiyansa
FIR’AUNA AKHANATEN
Babban dalilin da ya sa na zabi in kawo bayani akan wannan Fir’auna shi ne, domin ya bambanta da saura. A baya mun gaya maku cewa, Misrawa na bautawa Iyayen giji da dama, babba a cikinsu kuwa shi ne Amun-Re. Fir’auna Amenophis III, shi ne mahaifin Fir’auna Amenophis IV. Mahaifiyar Amenophis IV kuma Sarauniyar Amenophis III sunanta Tiye. Amenophis III Basarake ne wanda ya yi fice ya kuma yi suna ta fuskar jarumtaka da mulki.

Lokacin da Amenophis IV yana yaro, watau yana dan Sarki kenan, bai taso tamkar sauran ‘yan Sarki ba. Maimakon ya maida hankali wurin koyon dabarun yaki da kuma sauran al’amura na jarumtaka da mulki, shi ya fi damuwa ne da wasu abubuwa na dabam. Misali shi ya fi damuwa da halittun Ubangiji madaukaki. Ya fi damuwa da kallon Dinya da Agwagin ruwa ko kifaye. Ya fi damuwa da kallon fitowar rana da faduwarta. Da sauran abubuwa na halitta.

A wannan lokaci, manyan malaman addini na Masar wadanda ke zaune a birnin Thebes sun kasaita matukar gaske. Tun farkon farawar Sabuwar Masaurauta, su wadannan malamai kan sami dukiya mai yawa daga masu sarauta da kuma mutanen gari. Saboda haka, sai suka fara zama barazana ga Fir’auna Amenophis III. Wannan ya sa a lokacin ya fara tunanin yaya zai yi ya rage masu karfi. Ta haka ne ya fara gina manyan Mutum-mutumansa wadanda daga bisani ya fara jan hankalin a rika bauta musu. Ta haka kenan ya fara janye mabiya Amun-Re kenan. A Birnin Thebes bautar Fir’auna ta fara karbuwa sosai haka a kudancin Masar.

Lokacin da Amenophis IV ya zama Sarki, ya gaji mahaifinsa Amenophis III, sai ya fara nuna alamun yana da ra’ayin wani Ubangiji da ake kira Aten. Shi wannan Ubangiji ba shi da mabiya da yawa. A takaice ma dai, ba a damu da bin wannan Ubangiji Aten ba. Ana cikin haka sai ya far a nisanta kansa daga bautar Ubangiji Amun (Amun-Re). Daga nan sai ya gina Mabautar Aten a Birnin Karnak, Sarauniya kuma Uwa Tiye ta rika tausawa danta domin lura da cewa shi mutum ne wanda bai damu da duniya ba, kuma ga alama ba zai iya yin mulki yadda ya kamata ba, ta hanyar yin amfani da karfin tuwo. Ba a tabbatar da cewa ko ta goyi bayansa ba bayan ya bayyana sabon ra’ayinsa na jaddada addinin Aten.

A takaice dai sai ya bayyanawa Misrawa cewa ya sauya sunansa daga Amunophis zuwa Akhanaten. Wanna sabon suna ya warware shi daga bautar Amun gaba daya ya kuma lika shi da bautar Aten. Ma’anar sabon sunansa shine Aten ya wadatu da ni. To daga nan ne ya fara bayyana cewa Misrawa su daina bautar Iyayen giji barkatai. Su bautawa sabon Ubangijinsa watau Aten. A cewarsa Aten shi kadai za a bautawa kuma ba za a wakiltar da siffarsa ta hanyar gunkin mutum ko dabba ba. Shi kuma Akhanaten ba za a kira shi ko a bauta masa a matsayin Ubangiji ba. Duk wannan abu da ake yi mabiya Amun-Re ba su jin dadi. Don haka sai suka fara shirya masa makarkashiya. Wannan ne ya sa ya yi hijira daga Thebes zuwa wani wuri tsakanin ta da Memphis (wani babban birni a Masar ta dauri). A daidai wannan lokaci ne ya auri wata mata mai suna Nafertiti, ba a da tabbacin ko ita wacece ko ‘yar wacece, sai dai ana kyautata zaton cewa kila ‘yar sarauta ce ita ma. Nafertiti ta yi imani da wannan sabon addini na mijinta ta kuma ba shi cikakken goyon baya.
Surar matar Akhenaten Nefertiti
A cikin shekar sa ta shida ne a kan karaga ya tafi wurin da zai gina sabon birninsa wanda ya kira Birnin Ubangiji. A dai-dai inda ya tsaya don kafa wannan sabon birni, ba komai face wasu ‘yan gidajen da talakawa ke zaune ciki bakin gabar kogin Nilu. Akhanaten da kansa ya ce game da wurin “Na sami wannan wuri da bamallakar kowa ba, ba na wani Ubangiji ko Uwargijiya ba ne, ba na wani yarima ko gimbiya ba ne, ba wanda zai ce nasa ne” Ya kwana a tantinsa, da safe ya fito ya shata iyacin inda birnin zai tsaya, ya kuma sa masa suna watau AKHATATEN ma’ana Birnin Aten. Sannan ya yi bauta ga Ubangijinsa, bayan nan sai ya cewa wadanda suke biye da shi “ Aten Ubangiji ne, shi ne ya umarce ni da in gina wannan birni” sannan ya ci gaba “Ga ubangiji na Aten zan gina wuraren bauta”

Bayan shekara biyu aka kamala ginin Akhataten suka dawo tare da iyalinsa da mabiyansa. Bayanan da aka samu sun nuna cewa, wasu sun biyo shi ne domin sun yi imani da shi, wasu kuma don su sami abin duniya suka yi kaura tare da shi. Imaninsa da gaskiya watau Maat ya bambanta da na sauran Fir’aunoni da suka gabace shi. Ga Akhanaten, Maat ba kawai tana nufin gaskiya tsurarta ba ne kawai, a’a, in an ce Maat, ana nufin ne aikata gaskiya, barin munafunci da annamimanci, bayyan abubuwa a yadda suke. Wannan sabuwar manufa ta shafi yadda ake tafiyar da rayuwar yau da kullum ta wancan zamani. Ga kadan daga cikin yadda yake yabon Ubangijinsa Aten. (daga cikin rubuce-rubucensa)

Ayyukanka suna da yawa matuka
Ya ubangiji tilo, babu wani tamkar sa
Kai ka hallici duniya yadda ka so
Da kai kadai ne tilo,
Duk mutum, duka dabbobi na gida da na dawa
Duk hallitta mai tafiya bias dugaduganta
Duk abubuwan dake sama da halittu masu fiffika suna tashi
(shi Ya halicce su)

Kai ka halicci kasashe har da kasar Masar
Ka ajiye kowane mutum a wuri nasa daban
Al’umomi suna harsuna da-ban daban
Siffarsu ta jiki da launi sun banbanta
Domin ka banbance tsakaninsu.

Ya haifi diya mata kamar su Merytaten da Meketaten da Ankhhesenaten, sai dai bai haifi namiji ba.

Mabiya Iyayen giji da yawa sun ci gaba da shirya masa kulle-kulle da har daga baya dai ya sami baraka da matarsa suka rabu. Daga bisani ya zabi mijin diyarsa Makataten watau Samenkhkare ya zamar masa waziri. Da ga bisani dai ba za a iya cewa ga yadda ya kare ba. To amma bayan fakuwarsa Semenkhkare ya zama Sarki. Bayan ya zama sarki sai ya bar Akhataten ya koma Thebes. Shi ma daga nan ba a san yadda ya kare ba. Tutankhaten wanda shi ma surukin Akhanaten ne shi aka nada sabon sarki, sai dai yana yaro sosai. Don haka, Ay wani babban kwamadan Akhanaten kuma mai bin addininsa shi ke mulki. Tutankhaten wanda ya maida sunansa Tutankhamun, bai dade yana kan sarauta ya mutu yana dan shekara 18. Don haka Ay ya haye karagar mulki. Shi ma saboda tsufa bai dade ba ya mutu. Daga nan sai sarauta ta fada hannun Horembeb, wani babban kwamandan Masar.

Horembeb ya tabbatar da cewa an koma kan tafarkin addini da ake bi kaka-da kakanni. Da yake soja ne, sai ya dora kasar akan tsarin mulki irin na soja. Ya fara mulkin kama karya da gallazawa talakawa, tare da hukunce-hukunce marasa tausasawa. Kamar guture hancin mutum in ya karya dokar kasa. Ya sa aka goge duk inda sunan Aten ko Akhanaten ya fito a Masar saboda a manta da shi har abada. A shekarar 1320BC ya mutu, daga nan Gidan Sarauta na 18 ya zo karshe. Horembeb ba shi da magaji, saboda haka sai sarauta ta fada hannun wani mayakinsa mai suna Paramesses. Wannan shi ne kakan kakan Fir’aunan Annabi Musa (AS). Ya cire Pa daga sunansa ya koma Remesses I.

FIR’AUNA REMESSES II
Ramesses II dai shi ne wanda ake kyautata zatin cewa shi ne Fir’aunan da ya yi zamani da Annabi Musa (AS), wanda Allah Ya fadi tarihinsa a cikin Alkur’ani, littafin Allah mai tsarki. Kodayake masana irin su Maurice Bucaille suna ganin Merneptah ne ba Ramesses II ba. Saboda haka, ra’ayi ya banbanta ko tskanin Ramesses II da Merenptah wanene Fir’aunan Annabi Musa (AS). Wasu masanan Masar tadauri na ganin cewa Annabi Musa (AS) ya yi yayi da Remesses II ya kuma yi yayi da Merenmptah, wasu kuma na ganin dai-dai lokacin da Yahudawa suka yi kaura daga Masar suka bi ta kogin Maliya, Merneptah ne ke kan karagar mulki. Sai dai ba bu cikakken bayani akan shi Merneptah kamar yadda ake da bayani akan Remesses II. To, kowane ne dai daga cikinsu Fir’aunan Annabi Musa (AS) Allah ne Ya fi tokowa sani. To amma dai duka gawawwakin na su suna nan, don haka, alkawarin Allah Ya cika kenan. A duba shafi na gaba domin ganin kyamkyamammun gawarwakin Remesses II da Merneptah
Idan mun dauka Remesses ne Fir’aunan annabi Musa (AS) to, kusan duk mai bin addinin Muslunci ko na Kiristanci ko Yahudu ya karanta a cikin littafinsu yadda Allah Ya bada labarin kafircin Fir’auna Remesses II. Saboda haka, ba za mu yi wani dogon bayani ba illa dan tsokaci. Shi dai Remesses II da ne ga Seti I wanda shi kuma da ne ga Remesses I. Remesses I da sunansa Paramesses wanda asali ba jinin sarauta ba ne. Shi soja ne wanda ya gaji mulki Misra daga hannun Fir’auna Horembeb. Ya yi yake-yake da gine-gine manya katafarai. A takaice dai za a iya cewa yana daya cikin manyan masu mulki da Masar ta dauri ta taba yi. Cikin katafaraen gine-gine da yayi, ana daukar babban dakin nan da girmansa ya kai murabba’in kafa 5800 kuma an yi masa rufi tsaf. A yau da yake a bude, in ka shiga ka ce a wani sararin daji kake. Har yau in ka ie Karnak da Abu Simbel za ka ga wasu daga cikin maka-makan gine-gine da ya yi. Cikin manyan matansa akwai Nefertari da Manefrure. Ya kuma auri uwarsa ya kuma
aure diyansa mata guda uk`u. diyansa sun kai 150, dansa na 13 ne ya gaje shi shi. Sunansa Merneptah.
A shekarar 1881 aka gane kyankyamammun gawarwakin wasu fitattun sarakunan Masar ta dauri na Sabuwar Masarauta a wani wuri da yanzu akan kira Kufadar Sarakuna watau Valley of the kings. Cikin gawarwakin har da ta Fir’auna Remesses II, saura sune Seti I da Ramesses I da Ahmose I da Amenhotep I da Thutmose I da Thutmose II da kuma Thutmose III. Duka sai aka kai su gidan adana kayan tarihi na Masar. A cikin shekarar 1912 Masanin Masar ta dauri Eliot Smith dan kasar Ingila, ya fahimci cewa wata cuta ta kama gawar Remesses II saboda haka aka fara kokarin tsayar da kwayar cutar dake neman bata gawar. A cikin shekarar 1976 aka dauki gawar zuwa kasar Faransa don kyautata ta. Wannan shi ne karo na farko da gawar wani Fir’auna ta bar Masar. Da aka sauka da gawar a filin jirgin saman Orly, sai hukumomin Faransa suka yi mata tarba irin wadda ake yi wa Shugabannin {asashe har da shimfida jar darduma. Gawar Fir’auna Remesses II ta yi shekaru 3200 da binnewa, saboda haka ta fara fita daga hayyacinta. Don haka ne aka sa likitoci da masana kimiyya guda 102 karkashin Farfesa Lionel Balout suka yi watanni bakwai suna aiki akan gawar. Bayan an gyatta ta sai aka maido ta Masar. Ai alkawarin Allah ba ya tashi.
KAMMALAWA
A wurin kammalawa, ina ganin zai yi kyau in yi bayani a takaice bisa yadda ilmin Masar ta dauri ya iso mana. A nan ya kamata a fahimta cewa hanya ta farko ita ce ta Saukakkun Litttatafai kamar Al-qur’ani mai tsarki. Hanya ta biyu ita ce ta hanyar abubuwan tarihi da su Misrawan suka bar mana. Sai kuma hanya ta uku wadda ita ce ta bada cikakken bayani akan tarihin wayewar kan Masar ta dauri na tsawon shekaru dubu biyar zuwa bakwai. Wannan ita ce ta hanyar iya karanta, da fahimta da kuma fassara rubutunsu na dauri. A nan ya kyautu mu koma mu yi godiya ga masana na baya da suka yi kokarin gano sihirin rubutun misrawan dauri, irin su Nicolas Claude Fabri da Athanasius Kircher da Bernard Montfaucon da Jean-jacques Barthelemy da Antione Isaac Silvetre. To amma mutum daya da za mu fi yi wa godiya shi ne dan kasar Faransa Jean-Francois Champollion wanda ya shekara 30 yana kokarin warware zaren ya kuma warware shi a karshe. Sai kuma masanan Masar ta dauri da dama da suka yi bincike da rubuce rubuce a kan Wayewar kan Masar ta dauri irin su Manetho da Herodotus da Lepsius da Maspero da Marriette da Carter da Cheik Anta-Diop da su Gardiner da sauransu. Babu shakka, ba dominsu ba, da sai mu ce sai dai a yi kame-kame da shaci-fadi.

To, babban abin burgewa da Masar ta dauri ta barwa ‘yan baya shi ne gine-gine. Duk da cewa su gine-ginen duwatsu suka yi, za mu iya cewa Misrawan dauri da na yau sun yi kokarin adana kayan tarihinsu, ba domin haka ba, da babu abin da zai rayu har mu ‘yan baya mu zo mu gane shi mu kuma karu da shi. Don haka, kenan ya zama wajibi ga kowace irin wayewar kai ta adana kayan tarihinta domin ‘yan baya. Wannan ne ya sa na ga ya dace in nuna bakin cikina game da yadda mu a kasar Hausa muke yin watsi tare da fatali da kayan mu na tarihi. Yanzu ku duba badalar Kano. Duk da cewa an gina ta ne lokacin sarakunan Habe, da jahadi ya zo karkashin Fulani, ba su rusa ta ba. Da Turawa suka zo, ba su rusa ta ba. Amma bayan Turawa sun tafi, gata nan ta zama abin tausayi. Na tabbata nan da ‘yan shekaru ba za sami ko kufai na badala ba (sai shaguna?). Don haka, ina ganin lokaci ya yi da mutanen Kano za su fara wani motsi ko rugugi babba na gani cewa an tada badalar Kano. Kada ku ji komai, za a iya. Ku kuma daliban Jami’a, hakkin ku ne ku wayar da kan jama’a akan wannan harkar. Zan dakata anan sai kuma in mun sami wata dama za mu dora. Na gode kwarai da kuka zo kuka saurare ni.

6 comments:

Anonymous said...

gasuwa da fatan malam yana lafiya

naji dadi sosai dana fara ganin shafin yanar gizo da hausa babu shakka wannan ci gabane, kuma ina fatan za'aci gaba rubuto mana maqalat da zasu haskaka mana hanyoyin mu susa mygyara tafiyarmu musan addini da dunya da tarihin al'ummar mu?

malam ina da tambaya?

ko akai wani littafi da yake magana akan musulman garuruwan hausa kafin khilafar-al-othmaniyyah,
anan inda nake yanzu anata sabani kan haka, shine nakeso nasmain bayanin mai warkarwa bisa hakan

idan babu

ina rokon kayi mana bahsi, akan maudu'in, domin musan tarihin mu ,wanda muka rubuta da hannunmu

nagode se mun jika
akhuka fillah
mustapha barnoma

Yusuf M. Adamu said...

adMalam Barnoma na ji dadin ganin sharhinka duk da cewa ban gani da wuri ba, Dangane da garuruwa Musulmi kafi kafuwar daular ban gane wacce ka ke nufi ba, kani nufin Ottoman Empire ko Daular Sakkwato?

Anonymous said...

tagarduniya.blogspot.com is very informative. The article is very professionally written. I enjoy reading tagarduniya.blogspot.com every day.

Anonymous said...

I would like to exchange links with your site www.blogger.com
Is this possible?

Anonymous said...

I should digg your article therefore more people can see it, really helpful, I had a hard time finding the results searching on the web, thanks.

- Thomas

AHMAD IBRAHIM AHMAD said...

Gud work

  • Locations of visitors to this page

Blog Archive

About Me

My photo
Kano, Kano, Nigeria
Dr. Yusuf M. Adamu, Fulbright Fellow, member, Nigerian Academy of Letters and Fellow of the Association of Nigerian Authors is a Professor of Medical Geography at the Bayero University Kano. He is a bilingual writer, a poet, and writes for children. He is interested in photography and run a photo blog (www.hausa.aminus3.com) All the blogs he run are largely for his hobbies and not his academic interests. Hope you enjoy the blogs.